Rashin tabbatar da kujerata bai dame ni ba – Ibrahim Magu

Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu,  ya bayanna cewar ba shi da wata damuwa kan matsayin da Majalisar Dattawa ta dauka na rashin tabbatar da shi a kan mukaminsa. Magu yayi wannan furuci ne a lokacin da yake  tattaunawa  da jaridar Daily Trust a Abuja.

Magu ya kara da cewa, “A duk lokacin da aka dora maka alhakin wani aiki, abin bukata a gareka shine, mayar da hankali kan wannan aiki, kar kuma ka yi tunanin cewa kowa ne kan gamsu da kokarin ka ko bajintar ka”. Ibrahim ya kara da cewa “Sa’ilin da ka yarjewa kan ka cewar abinda kake yi daidai ne, to lallai ka dau turbar ci gaba kenan. Ni wannan abu da su ka yi bai dame ni ba ko daya”.

Magu ya kara da cewar bayanai na karya da masu bankade da tono asiri kan yi na karya, na zubar da mutuncin hukumar.

“Muna amfani da bayanan da akan samu sosai, amma wasu lokatan sai a tarar da cewa ba komai idan ka je bincike. Saboda haka, muna yin taka-tsantsan kafin mu dira a waje a halin yanzu” inji Ibrahim Magu.

 

 

Asalin Labari:

dailyTrust, Muryar Arewa

1771total visits,2visits today


Karanta:  Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami'anta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.