Real Madrid Za Ta Kara Da Fiorentina

Kungiyar Real Madrid za ta fafata da Fiorentina a gasar Santiago Bernabeu Trophy a ranar Laraba.

Madrid ta ci kofin sau 11 a jere, kuma rabon da a doke ta a wasannin tun 2004, sannan ta lashe shi sau 26 jumulla.

Wannan karawar da Madrid za ta yi da Fiorentina ita ce ta 38 a gasar, kuma cikin ‘yan wasan da suke buga mata tamaula su biyar a yanzu sun ci mata kwallaye a fafatawar.

‘Yan wasan sun hada da Benzema wanda ya ci biyar da Ramos da Nacho kowannnensu ya ci biyu-biyu sai Marcelo da kuma Isco da suka ci dai-dai.

Tun bayan da Madrid ta yi rashin nasara a hannun Pumas a gasar, ta ci hadakar ‘yan wasan da ke buga gasar Amurka da Anderlecht da Partizan da Sporting Clube na Portugal da Rosenborg da Penarol da Millonarios da Al-Sadd da Galatasaray sau biyu da kuma Stade de Reims.

Ga jerin ‘kungiyoyin da suka lashe kofin:

  • Real Madrid 26
  • Bayern Munich 3
  • Milan 2
  • Inter 2
  • Hamburg 1
  • Dynamo Kiev 1
  • Ajax 1
  • Pumas 1
Asalin Labari:

BBC Hausa

780total visits,1visits today


Karanta:  ''Ozil bai damu da batun komawa United ba''

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.