Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona

Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu na Spanish Super Cup a ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Wasan farko da aka yi a a gasar a Nou Camp, Real ce ta yi nasara da cin kwallaye 3-1, kuma a karawar ce aka bai wa Cristiano jan kati.

Wannan ne karo na uku da kungiyoyin za su fafata a wasan hamayya da ake yi wa kirari da sunan El Classico a bana.

Barcelona ta ci Madrid 3-2 a International Champions Cup a Amurka a wasannin atisayen tunkakar kakar bana, kuma ita ce ta lashe kofin.

Barcelona ta dauki Spanish Super Cup sau 12, yayin da Real Madrid keda shi tara, an kuma fara wasannin a 1982, kuma Real Sociedad ce ta fara dauka.

Asalin Labari:

BBC Hausa

954total visits,4visits today


Karanta:  Zinedine Zidane zai tsawaita zamansa a Madrid

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.