Rikici ya barke tsakanin al’ummar Hausawa a Lagos

Rahotannin daga jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya na cewa wani rikici ya barke a tsakanin al’ummar Hausawa da ke a babbar kasuwa ta Alabaraho.

Wasu rahotanni na cewa an garzaya da mutum takwas asibiti wadanda aka raunata.

Rikicin dai ya taso bayan kokarin da ake a sasanta tsakanin wasu sassa biyu da basa ga-maciji da juna a kan wanene shugaban kasuwar Alabaroho.

Tuni dai aka tura jami’an tsaro na ‘yan sanda. Amma har yanzu ‘yan sanda ba su ce komai ba kan batun.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1494total visits,1visits today


Karanta:  Kotu Ta Mallakawa Gwamnatin Najeriya Wasu Gidajen Mrs Madueke dake Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.