Rikici ya barke tsakanin al’ummar Hausawa a Lagos

Rahotannin da mu ke samu na cewa wani mummunan rikici ya barke a tsakanin al'ummar Hausawa da ke a babbar kasuwa ta Alaba Rago.

Wasu rahotanni na cewa an sassari mutum takwas da raunata wasu da dama.

Rikicin dai ya taso bayan kokarin da ake a sasanta tsakanin wasu sassa biyu da basa ga-maciji da juna a kan wanene shugaban kasuwar Alaba rago.

Tuni dai aka tura jami’an tsaro na ‘yan sanda.

Za mu kawo muku karin bayani nan gaba kadan.

Sanarwar da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta ce rufe kasuwar na wucin gadi ne domin kawo karshen tashin hankalin da aka samu.

Matakin na gwamnan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin ‘Area Boys’ wadanda galibinsu Yarbawa ne, da kuma ‘yan acaba wadanda galibinsu Hausawa ne ‘yan arewacin kasar.

Wasu rahotanni sun ce an halaka akalla mutane uku a rikicin wanda aka soma shi tun a ranar Talata.

Wakilinmu na Lagos ya ce an tura karin jami’an tsaro domin kwantar da lamarin.

Rikicin Kabilanci wani al’amari ne da yake addabar sassa daban-daban na Najeriya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1011total visits,1visits today


Karanta:  Gwamnati Ta Dukufa Wajen Ceto Mutanen Da Aka Sace a Borno - Osinbajo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.