Rikicin sakamakon zabe ya yi sanadin rai 4 a Kenya

Rahotanni Daga kasar Kenya sun ce mutane 4 aka kashe a tashin hankalin da ya biyo bayan kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar wanda ‘yan adawa ke zargin an tafka magudi.

 

 

 

 

 

 

Bada sakamakon wucin gadi cewar shugaba Uhuru Kenyatta ke gaba wajen lashe zaben da kashi 54 ya haifar da cacar baki, inda ‘yan adawa tare da dan takarar su Raila Odinga mai kashi kusan 45 suka kekashe kasa cewar basu amince da sakamakon ba saboda an tafka magudi.

Wannan zargi ya bai wa magoya bayan Odinga fara zanga-zanga da kuma arangama da jami’an tsaro wadanda nan take suka harbe mutane 2 har lahira bayan sun tare hanya suna kona tayun mota.

Shugaban ‘Yan Sandan Nairobi Japheth Koome ya ce mutanen biyu da aka kashe sun kai hari ne kan jami’an su.

Larry Kieng, shugaban ‘Yan Sandan Yankin Tana ya ce jami’an sa sun kashe mutane biyu da suka kai musu hari.

Tuni shugaban hukumar zabe Ezra Chiloba ya karyata zargin magudin da ‘yan adawar suka yi.

Suma masu sa ido a zaben, karkashin John Kerry, tsohon Sakataren harkokin wajen Amurka sun bayyana gamsuwar su da yadda zaben ya gudana.

Asalin Labari:

RFI Hausa

1610total visits,1visits today


Karanta:  Turkiyya ta saki sautin kisan Kashoggi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.