Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun Ta Damke Wasu Bata Gari 26

'Yan sanda a jihar Osun sun samu nasarar kama masu aikata laifuffuka 26, ciki harda wanda yayi karyar cewa shi mace ce ta yanar gizo.

Runduanar ‘yan sandan jihar Osun, ta kama kuma ta gabatarwa taron yan jarida wadansu masu aikata laifuffuka 26 da suka harda da masu sata da garkuwa da mutane, da masu fashi da makami da wadanda suka kware wajen satar motoci da Babura da kuma wani wanda yayi shigar mata. Yace shi mace ce ta yanar gizo, har ya samu nasarar damfarar wani Ba’amerike batura dala dubu 80.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun Mr. Femi Oyeleye. Shi ya gabatarwa ‘yan jarida wadannan bata gari, a birnin Oshogbo baban birnin jihar Osun.

Yace wanda ya damfari Ba’ameriken ya gabatar da kansa a zaman mace ta yanar gizo, har ya samu nasarar dafarar baturen, daya sa masa kudin a asusu ajiyarsa na baki.

Kwamishinan yan sanda yace irin wannan zamba ke bata sunan Nigeria.

Asalin Labari:

VOA Hausa

505total visits,1visits today


Karanta:  'Yan Sanda Sun Koka Bisa Yawaitar Aikata Fyade a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.