Samar Da Aikin Yi a Yankunan Igbo Zai Iya Kawo Zaman Lafiya – Kwararru

Bayan da babbar kotun tarayyar Najeriya ta bai wa gwamnatin kasar ikon ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta’addanci. Mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnati ta samar wa da matasan kungiyar aikin yi don samar da zaman lafiya.

An yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta tsara ingantacciyar hanyar samarwa ‘yan kungiyar IPOB aikin yi, don magance illolin dake tattare da zaman banza.

Yayin da Muryar Amurka ta zanta da wasu mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, da akwai alamar cewa batun rashin aikin yi shine ya mamaye yankin ya kuma haddasa damuwa ga al’ummar.

A cewar Dakta Stanly Okereke, wanda ke zama babban malami mai kula da harkokin dalibai a jami’ar jihar Abia, na ganin idan har gwamnatin ta samarwa da al’umma isasshiyar wutar lantarki za ta cimma buri, saboda matasa kan iya amfani da wutar lantarki wajen yin wasu sana’o’i don dogaro da kai.

Shi kuma wani malami mai koyar da kimiyyar harsuna da lamuran yada labarai, Dakta Cimma, na ganin rashin kulawa ne ya janyo irin wannan zanga-zangar da kuma kafa kungiyoyi irin su IPOB.

Amma babbar tambaya ita ce ta wacce hanya ce ya kamata a bullowa lamarin, kasancewar a baya an taba yin irin wannan zanga-zanga a yankin Kudu maso Kudu da kuma yadda aka magance ta.

Ya ce dole sai gwamnatin tarayya ta samar da ingantacciyar hanyar tsara wani shiri da zai taimakawa matasan yankin domin samar da zaman lafiya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

835total visits,1visits today


Karanta:  'Sojoji Sun Kai Samame Gidan Jagoran Biafra'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.