Sarkin Musulmi Ya Jaddada Mahimancin Zaman Lafiya

A jawabinsa wa al'ummar Musulmi bayan saukowa daga babbar sallah, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya tabo batun rarrabuwan kawunan 'yan Najeriya da barazanar da hakan ke yiwa kasar kana ya jaddada mahimmancin zaman lafiya.

Babban abun da ya fi daukan hankalin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III a jawabinsa na babban sallah wa Musulman Najeriya shi ne irin halin da kasar Najeriya ke ciki da kalubalen rarrabuwan kawunan ‘yan kasar.

Yana mai cewa kwanakin baya an samu kalamun rarrabuwa daga mutane daban daban daga sassan kasar. Ana cewa mutane su bar inda suke su koma wurarensu na asali. Yace an fadi hakan a arewa an kuma fada a kudu.

Sarkin Musulmin ya jaddada mahimmancin zaman lafiya da hadin kai wanda yace shi ne kawai tafarkin samar da cigaban kasa. Yace a zauna lafiya da kowa a kuma girmama juna saboda “Allah ne Ya hadamu wuri guda”. Ya kira da a gujewa tashin hankali saboda ba zai haifar da da mai ido ba. Zaman lafiya ya fi zama dan sarki.

Sarkin Musulmi ya kuma yi tsokaci akan matsalolin da ‘yan gida da baki ke fuskanta inda yace kowane dan Najeriya na da damar zama duk inda ya zaba ya zauna a kasar. Ya kira a yi koyi da jihar Sokoto inda ‘yan asalin kasar ke zaune lafiya da wadanda suka fito daga wasu jihohin.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1083total visits,2visits today


Karanta:  Sojin Nigeria 'sun kai samame' ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.