Sarkin Musulmi Ya Kira A Mayar da Hankali Wajen Inganta Tattalin Arziki

Sarkin Muslmi Sultan Sa'ad Abubakar ya yi kira a Minna da a mayar da hankali akan habaka tattalin arziki domin inganta rayuwar al'umma da zata sa mutane ba zasu damu da wake shugabancin kasar ba.

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Sultan Sa’ad Muhammad Abubakar ya yi kira da a maida hankali wajen bunkasa tattalin arziki da zai sa ‘yan kasar su kasance cikin walwala.

Yayinda yake jawabi a wani taron bunkasa kasuwanci a Minna babban birnin jihar Neja yana mai cewa kamata yayi ‘yan Najeriya su maida hankali wajen kiran a yi kokarin bunkasa tattalin arziki.

Inji Sarkin, “na yi imani idan muka maida hankali wajen yin magana akan a bunkasa tattalin arziki zai taimaka domin kuwa idan tattalin arziki na tafiya yadda ya kamata babu wanda zai damu da wa yake mulkin wani”

Mai sharhi kan alamuran kasa kuma shugaban cibiyar bincike da nazarin al’adun kimiya da fasaha dake Minna Ahmed Ibrahim Khalil yace maganar Sarkin Musulmi tana kan hanya “to amma akwai wani hanzari ba gudu ba”

Yana mai cewa matsalar Najeriya ba ta tattalin arziki ba ne ta rashin shugabanci ne saboda babu iyaye. A da can baya ana anfani da shugabannin gargajiya da na addinai amma yanzu an ciresu daga harkokin kasar, inji Khalil. A cewarsa kowa ya yi kudi yanzu shi ma sarki ne.

Asalin Labari:

VOA Hausa

567total visits,2visits today


Karanta:  Nijeriya Za Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya Mai Manufa Guda…. – Sultan

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.