Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin sayar da takardun lamuni na Sukuk wadanda babu kudin ruwa a kansu. Hukumar da ke kula da basuka ta kasar (DMO) ce za ta kadddar da shirin, wanda aka ware kimanin naira biliyan 100. A cewar jami’ai, wannan shiri zai taimaka wurin samar da […]

Nigeria na Cikin Halin Murmurewa – Farfesa Sheka

Wani masanin tattalin arziki a Nijeriya, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce tattalin arzikin Nijeriya na tafiyar hawainiya bayan hukumar kididdiga ta ce kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta yi fama da shi.

Nigeria na Cikin Halin Murmurewa – Farfesa Sheka

Masanin ya ce idan tattalin arziki yana bunkasa da kashi daya ko biyu ko uku, to hakan na nufin yana tafiyar hawainiya kenan, “wanda shi ma matsala ce”. Wani rahoto da Hukumar Kididdiga a Nijeriya ta fitar ne ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada. Rahoton ya ce tattalin […]

Farashin Ragunan Layya Sunyi Tashin Gwauron Zabbi

Yanzu haka Jamaa sun fara kokawa game da farashin ragunan layya, da yawan jamaa na cewa ko baya ga tashin farashin raguna haka kuma kudi sunyi wahalar

Farashin Ragunan Layya Sunyi Tashin Gwauron Zabbi

Yanzu haka Jamaa sun fara kokawa game da farashin ragunan layya, da yawan jamaa na cewa ko baya ga tashin farashin raguna haka kuma kudi sunyi wahalar samu.Hatta suma masu sayar da ragunan sun koka akan rashin kasuwa. Yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke fara haramar shirye-shiryen sallar Layya – Yanzu haka farashin […]

Fatan ’yan kasuwar Kano kan tallafin gobara

Shugaban Hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar Sabon Gari, watau Amata Alhaji Ado Bilyaminu, wanda ya nuna jin dadinsa na kaddamar da wannan asusu, inda ya bayyana cewa ‘yan kasuwar Sabon Gari masu dimbin yawa sun yi mummunar asarar dukiyoyinsu wanda sakamakon wannan gobara da yawansu ba sa zuwa kasuwa, saboda komai nasu wuta ta cinye, kuma babu wani jarin da za su iya komawa kasuwanci.

Fatan ’yan kasuwar Kano kan tallafin gobara

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani asusu domin tara kudi don  tallafa wa ‘yan kasuwar da iftila’in gobara  ya shafa,  kuma a lokuta daban-daban  a kasuwanni guda biyar da ke jihar, watau kasuwar Sabon Gari da kasuwar Kurmi da kasuwar Singa kasuwar garin Gwarzo da kuma kasuwar sayar da wayoyin hannu da ke Farm Centre. […]

‘Ko Buhari Ya Tambaye Su Aikin Yi Nawa Aka Samar?’

Wasu masana tattalin arziki a Nijeriya, sun fara kalubalantar shugaban kasar Muhammadu Buhari game da farin cikin da ya nuna kan bayanin farfadowar tattalin arzikin da ministocinsa suka ce ya yi.

‘Ko Buhari Ya Tambaye Su Aikin Yi Nawa Aka Samar?’

Dr. Nazifi Darma ya ce kamata ya yi shugaban ya tambayi ministocinsa ko mutum nawa aka samarwa ayyukan yi sakamakon ci gaban da suke ikirarin (tattalin arzikin) kasar ta samu. “Ayyuka miliyan nawa aka samar?” “Kuma game masana’antun da suka durkushe, guda nawa ne suka bude suka ci gaba (da aiki). Kuma me suka sarrafa?”, […]

Dangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siga a Jihar Neja

Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja don gina katafaren kamfanin siga na kimanin Naira biliyan 166 a jihar.

Dangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siga a Jihar Neja

Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan  wata  yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja don gina katafaren kamfanin siga na kimanin Naira biliyan 166 a jihar. Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote shi da kansa ya sanya hannu a madadin kamfaninsa shi kuwa Gwamna  Abubakar Sani Bello ya sanya hannu a madadin jihar Neja. Da yake […]

Mai ya sa kasuwancin gawayi Yafi kowanne kasuwancin albarka

Me Yasa kasuwancin Gawayi Yafi Kowana Kasuwancin Albarka a jihar Kano. Saboda tashin karansin da gas yasa mutane da yawa suka raja’a da girki da aiki da gawayi.

Mai ya sa kasuwancin gawayi Yafi kowanne kasuwancin albarka

Tashin kalanzir da iskar gas ya sanya al’umma da dama sun raja’a da amfani da gawayi wajen girki. Wannan ya sanya mutane irinsu Mallan Isa Sagiru da ke zaune a unguwar Dorayi ya koma amfani da gawayi saboda ya taimaki kansa da kuma masu saida gawayi inda ya kara da cewar ya fi kowanne irin […]

Kasuwar hannayen jari ta Nigeria ta yi matukar bunkasa

Darajar kasuwar harkokin hannayen jari ta Najeriya na ci gaba da karuwa bayan ta samu bunkasar da ba ta yi kamarta ba a wata 33 da suka wuce ranar Talata.

Kasuwar hannayen jari ta Nigeria ta yi matukar bunkasa

Zuwa lokacin da aka rufe kasuwar ranar Laraba, darajar ta karu da kashi daya da digo ashirin da shida cikin dari idan aka kwatanta da ranar Talata. Wato yawan hada-hadar da aka yi ta karu daga 37,525.38 zuwa 37,999.56. Kwana shida kenan a jere darajar kasuwar na hauhawa, sakamakon daidaiton da aka samu a kasuwar […]

Etisalat Nigeria ya sauya suna zuwa 9Mobile

Etisalat Nigeria ya sauya suna zuwa 9Mobile

Kamfanin wayar sadarwa na Etisalat a Najeriya ya sauya suna zuwa 9Mobile, bayan hedikwatar kamfanin da ke Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shelar janye wa daga Najeriya. Hukumar da ke sa ido a kan harkar sadarwa a kasar (NCC) ta bayyana amincewarta da sauya sunan a hukumance. Kamfanin na 9Mobile ya ce duk da cewa […]