Snapchat Ta Toshe Al-Jazeera A Saudiyya

Kafar sadarwa ta Snapchat ta toshe kafar yada labarai ta Al Jazeera a kasar Saudiyya.

Snapchat Ta Toshe Al-Jazeera A Saudiyya

Snapchat ya dauki matakin ne bisa umarnin da hukumomin Saudiyya suka ba da na cire baki daya kafar yada labaran mallakar kasar Qatar, saboda kasar ta bijirewa umarnin kasashen Labarawa da ke yankin Gulf da hakan ya sabawa dokokin kasashen. Qatar dai na takun saka da Saudiyya da wasu kasashen Larabawa da suka hada da […]

An kama ‘babban kwamandan IS’ a Kano

Hukumoni a Najeriya sun ce sun kama babban kwamandan kungiyar IS reshen yankin Afirka ta yamman wanda ya kisa kai wa Musulmi hari lokacin bukukuwan babbar sallah.

An kama ‘babban kwamandan IS’ a Kano

Hukumar binciken farin kaya ta kasar (DSS) ta ce kungiyar masu tada kayar baya ta IS reshen yammacin Afirka (ISWA) ta shirya ta da zaune tsaye lokacin bukukuwan sallah wanda aka yi a makon jiya. Kungiyar ta shirya kai hare-hare a jihohin Kano da Kaduna da Neja da Bauchi da Yobe da Borno da kuma […]

Kotun Koli ta Kenya ta rushe zaben Shugaban Kasa

Kotun Koli ta Kenya ta rushe zaben Shugaban Kasa

Kotun Koli a kasar Kenya ta rushe zaben da aka gudanar a kasar Kenya wanda shugaba Uhuru Kenyatta ya lashe inda ta umarci da a sake gabatar da sabon zabe nan da kwanaki 60 masu zuwa. Rushe zaben dai ya biyo bayan korafin da bangaren ‘yan adawa ya shigar karkashin jagorancin Raila Odinga wanda ya […]

Nijar ta Daure ‘Yan Sanda Uku Da Suka Ba Dalibi Kashi

Wata Kotu a Nijar ta yankewa wasu ‘Yan Sanda uku hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda samunsu da laifin dukan wani dalibin jami’a lokacin da dalibai ke gudanar da zanga zanga a Niamey.

Nijar ta Daure ‘Yan Sanda Uku Da Suka Ba Dalibi Kashi

Wata Kotu a Nijar ta yankewa wasu ‘Yan Sanda uku hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda samunsu da laifin dukan wani dalibin jami’a lokacin da dalibai ke gudanar da zanga zanga a Niamey. Kotun ta kuma umurci ‘Yan Sandan su biya tarra sefa miliyan 15 kwatankwacin yuro 23,000 ga dalibin da suka jikkata. […]

Niger: ‘Da Gangan Aka Kashe Dalibin Jami’a’ Mala Bagale’

Kwamitin da gwamnatin Jamhuriyar Niger ta kafa domin binciken sanadin mutuwar wani dalibin jami'a yayin wata tarzoma da jami'an tsaro ya fitar da rahotonsa.

Niger: ‘Da Gangan Aka Kashe Dalibin Jami’a’ Mala Bagale’

A watan Afrilu ne marigayi Mala Bagale dalibin jami’ar Abdou Moumini Dioffo da ke birnin Niamey ya mutu yayin wata zanga-zanga; a cikin wani yanayi da ya jawo takaddama kan abin ya yi sanadin mutuwarsa. Takwarorinsa dalibai dai sun ce sojoji ne suka harbe shi, yayin da jami’an gwamnati suka ce ya rasu ne sakamakon […]

Hadarin jirgin kasa ya halaka mutane 20 a Alexandria

Hadarin jirgin kasa ya halaka mutane 20 a Alexandria

Akalla mutane ashirin (20) sun rasa rayukan su da kuma wasu masu yawa da suka jikkata a wani hadarin jirgin kasa tsakanin wasu jiragen kasa guda biyu na fasinjoji a garin a kudancin Alkahira. Jirgin guda daya yana kan hanyar sa daga birnin Cairo, sai kuma dayan wanda ya taso daga Port Said inda sukayi […]

Koriya ta Arewa zata kai wa Amurka hari

Koriya ta Arewa zata kai wa Amurka hari

Koriya ta Arewa na shirin kai hari da makami mai linzami a kusa da garin Guam wanda yake karkashin kasar Amurka mai dauke da sojojin kasar ta Amurka dama wasu ma’adanai da kayan yaki a matsayin mayarwa da shugaba Donald Trump martani kan maganganun tashin hankula da yake yiwa kasar ta Koriya ta Arewa a […]

Gobara ta tashi a kurkukun Kuje na Abuja

Gobara ta tashi a kurkukun Kuje na Abuja

Wata gagarumar gobara wadda ta lashe gine-gine da yawa ta tashi a cikin kurkukun Kuje, dake Abuja. Gobarar wadda ta fara da misalin karfe 10:45 na safe, ta yi barna matuka. Wata kungiya wadda ta kira kanta da ‘Mai Yaki da rashin adalci kan fursunoni ta Najeriya (PAIN), ta dauki alhakin tashin gobarar. PAIN ta […]

NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

Hukumar Yakin da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) tare da sauran hukumomi sun sami nasarar kwace wasu haramtattun kwayoyi da yawansu ya kai kilogaram 881.100, sakamakon wani sumamen hadin gwiwa na musamman da aka gudanar a Jihar Sokoto da kuma wasu yankuna tsakanin bodar Najeriya da Nijar. Shugaban hukumar, Kanar Muhammad Mustapha Abdallah (Mai […]

1 2 3