Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama wani yaro mai shekara 14 wanda aka nuna a wani bidiyo yana taka rawar wakar 'Macarena' a kan titi.

Bidiyon ya ja hankulan dubban mutane a Twitter.

Hukumomi na yi wa yaron tambayoyi bayan an zarge shi da “nuna rashin tarbiyya” a birnin Jeddah, in ji wata sanarwa.

Ba a tabbatar da ko yaron dan kasar ta Saudiyya ne ba, kuma ko hukuma za ta gurfanar da shi a kotu.

A farkon wannan watan aka kama wani mawaki a kasar saboda ya yi rawar “dab” a yayin da yake waka a yankin kudu maso yammacin kasar,

A cikin bidiyon mai tsawon dakika 45, an ga yaron yana hana motoci wucewa a yayin da yake taka rawar wakar ta Macarena wadda ta yi tashe a shekarun 1990.

Ana ganin an saka bidiyon ne tun a watan Yulin bara.

@xmyd3

Saboda rashin rubutacciyar doka a Saudiyya, jami’ai da alkalai na da iko mai yawa wajen hukunta yara kanana a kasar mai bin tsattsauran ra’ayin addini.

Bidiyon ya raba hankulan masu ziyartar shafukan sada zumunta, inda wasu ke kare yaron, har suna kiransa “gwarzo”.

Wasu kuma sun soki halayyarsa, suna kiran abin da ya yi “rashin tarbiyya”.

Asalin Labari:

BBC Hausa

575total visits,1visits today


Karanta:  Za a kara yawan haruffan sakon Twitter

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.