Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Iran ta ce nan gaba kadan jami’an diflomasiyar kasashen biyu za su ziyarci Saudiya domin fahimtar juna a wani yunkuri na dinke sabani da barakar da ke tsakaninsu bayan sun yanke hulda a bara.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi ga daliban kasar, inda ya ce za a yi ziyarar ne bayan kammala aikin Hajjin bana.

Zarif ya ce tuni aka ba jami’an da za su gudanar da ziyarar iznin shiga kasashen, abin da suke jira kawai shi ne mataki na karshe da zai ba jami’an diflomasiyar kasashen biyu damar duba ofisoshin Jakadancinsu.

Wannan zai kasance karon farko da za a yi musayar jami’an diflomasiyasa tsakanin kasashen biyu tun 2016 da Iraniyawa suka abka ofishin jekadancin Saudiya bayan kisan malamin Shi’a.

Baya ga banbancin akida tsakaninsu, takaddama tsakanin kasashen biyu ta dauki shekaru yadda Saudiya da Iran ke kallon juna a matsayin wadda ke haifar da tashin hankali da kuma goyan bayan abokiyar hammayar.

Kasashen na da sabani akan rikicin Syria da Yemen, inda Iran ke marawa gwamnatin Assad da ‘Yan tawayen Huthi ‘Yan shi’a baya yayin da kuma Saudiya ke goyon bayan ‘Yan tawayen Syria da gwamnatin Yemen.

Asalin Labari:

RFI Hausa

785total visits,3visits today


Karanta:  'Yan Kasar Angola Sun Bukaci Dai Daito Tsakanin Attajirai Da Talakawa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.