Saudiyya Ta Bai Wa ‘yan Nigeria da Aka Ci Zarafinsu Diyyar N1m

Gwamnatin Saudiyya ta nemi afuwar wasu mahajjatan Najeriya biyu da jami'an tsaro suka ci zarafinsu a filin jirgin sama na Madina.

Mataimakin gwamnan yankin Madina, Sheikh Mohammad Albijawi, wanda ya mika wa wadanda abin ya shafa wasikar, ya tabbatar musu da cewar za a hukunta jami’an tsaron da suka aikata laifin.

Saudiyyar ta kuma bai wa mutanen diyyar riyal dubu biyar ga ko wanne daya daga cikinsu, wanda ya kama naira dubu 500 kenan ga duk mutum daya.

Ya yi kira ga mahajjatan Najeriya su kasance masu halayya mai kyau, kuma su gudanar da aikin hajin kamar yadda dokokin addini suka tanadar.

Ya bayyana cewar hukumomin Saudiyya sun samar da ababen more rayuwa da za su sa a gudanar da aikin hajjin bana ba tare da matsala ba.

Jakadan Najeriya a Saudiyya, Umaru Salisu, ya yaba wa hukumomin Saudiyya kan yadda suka mayar da martani game da lamarin cikin gaggawa.

Malam Uba Mana shi ne kakakin hukumar Alhazan Najeriya kuma dazu ta waya Suwaiba Ahmed ta tuntube shi dan jin karin bayani:

Da suke mayar da martani, mahajjatan da aka ci zarafinsu Audu Damina Muhammad da Ibrahim Nani Godi sun gode wa hukumomin Saudiyya da hukumar jin dadin alhajan Najeriya game da irin matakan da suka dauka kan abun da ya faru da su.

Sai dai ba a bayyana irin cin zarafin da aka yi wa mutanen ba.

Dama dai alhazai 79,000 ne hukumar jindadin alhazai ta ce za su sauke farali a bana.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1122total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.