Serena Williams ta haifi ‘ya mace

‘Yar wasan tennis da ta fi samun nasara a duniya a wannan zamani Serena Williams, ta haifi ‘yarta mace a wani asibiti da ke birnin Florida na Amurka.

Serena Williams, mai kimanin shekara 35 da haihuwa, ta samu juna biyun ne tare da farkanta Alexis Ohanian, bayan ta yi nasarar lashe wata babbar gasar duniya a karo na 23.

Alexis Ohanian, na daga cikin wadanda suka kafa wata kafar sada zumunta ta Reddit, wadda al’umma ke tattauna batutuwa ko labarai ko yin muhawara.

Serena Williams, sun hadu da farkan nata ne a Rome, bayan da ya gayyace ta zuwa wajensa.

Tuni dai ‘yan uwa da abokan arziki ke ta tura mata sakonnin taya murna.

A watan Afrilun da ya gabata ne, ‘yar wasan tennis din ta sanar da batun juna biyun da take dauke da shi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

573total visits,1visits today


Karanta:  Ba za mu yi kasadar neman Ronaldo ba – Mourinho

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.