An Gudanar da Jana’izar Kasimu Yero a Kaduna

An gudanar da jana’izar marigayi Alhaji Kasimu Yero a jiya bayan rasuwar sa a ranar Lahadin data gabata a gidan sa dake a unguwar Magajin Gari a birnin na Kaduna.

Alhaji Kasimu Yero mai shekaru 70 a duniya ya rasu a jiyan da rana a birnin Kaduna dake arewacin Najeriya bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Kasimu Yero ya kasance shahararren dan wasan kwaikwayo wanda ya yi fice ne a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen kafar yada labarai na kasa wato NTA, a wasannin Magana Jari Ce (na Hausa da na Turanci), Karanbana da dai sauransu.

Marigayi Kasimu Yero ya yi jinya ta wani lokaci mai tsaho inda a kwana kwanannan al’umma daga shiya daban daban suka dinga yin jerin gwano domin duba shi wanda ya hada da Sanata Shehu Sani na Kaduna.

 

Ana ci gaba da mika sakon ta’aziyya game da rasuwar dan wasan wanda ya shahara wajen barkwanci. Daga cikin wallafa sakon ta’aziyya sun hada da Hadiza Gabon, Ali Nuhu, Aminu Aliyu Shariff, Nura Hussain da dai sauran su a shafukan su na sada zumunta.

3639total visits,2visits today


Karanta:  Rashin lafiya: Jamila Nagudu ta gode wa masoyanta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.