Shettima zai jagoranci kwamitin fidda dan takarar gwamnan Anambara

Jam’iyyar APC ta kaddamar da kwamiti karkashin jagorancin Gwamna Kashim Shettima na Jihar Barno wanda zai gudanar da zaben fiidda dan takarar gwamna a zaben da z a a yi a jihar Anambara.

Zaben fidda gwanin wanda ’yan takara 12 ke neman tsayawa za a gudanar da shi ne a ranar Asabar 26 ga watan Agusta.
A hannu daya kuma jam’iyyar ta kafa kwamitin sauraren korafe-korafe karkashin jagorancin Dokta Hassan Lawal.
Sakataren shirye-shirye na Kasa na Jam’iyyar APC, Sanata Osita Izunaso shi ne ya kaddamar da kwamitocin biyu a jiya a Sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kaddamar da kwamitocin, Gwamna Shettima ya ce shi da kansa tare da shugaban sauraren korafe-korafe babu dan takarar da zai iya jan ra’ayinsu.

Ya bayyana cewa kwamitin a shirye yake ya gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya a jihar.

Da aka tambaye shi ko ta yiwu wani dan takara ya ja ra’ayinsa? Sai ya ce “Ku kalle ni, shin kun ga alamar farashi a jikina? Gaskiyar al’amari shi ne ina tare da dattijo wanda za mu yi aiki tare, Dokta Hassan Lawal shi ma babu alamar farashi a wuyansa shi ne shugaban kwamitin korafe-korafe. Za mu yi aiki tare a Anambara tare da tawagarsa”.

487total visits,1visits today


Karanta:  Hadaddiyar kungiyar matasan arewaci Nigeria ta janye umarnin korar yan kabilar Igbo bisa wasu sharudda

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.