Shi’a Ta Ki Tattaunawa Da Kwamitin Gwamnati a Najeriya

Kungiyar mabiya shi’a da ke Najeriya ta sanar da shirin kauracewa zaman tattaunawar kwamitin bincike da gwamnatin tarayyar ta kafa kan kisan mabiyanta sama da 300 da ake zargin sojin kasar da aikatawa.

Kungiyar ta ce la’akari da irin mutanen da aka zaba a kwamitin da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kafa na mutum 7, ba a shirya mata adalci ba.

Dambarwa dai ta faro ne tsakanin bangaren gwamnatin da kuma kungiyar ta Shi’a tun bayan wata hatsaniya data faru a karshen shekarar 2015 tsakanin dakarun sojin kasar da mabiyan lamarin daya kai ga asarar rayuka.

Ibrahim Musa Kakakin kungiyar mabiyar shi’ar ne a Najeriya, ya ce matukar ana bukatar su halarci zaman tattaunawar sai an yi biyayya ga ka’idojin da suka gindaya, ciki kuwa har da halartar jagoransu Ibrahim Zakzaky zaman tattaunawar.

Ibrahim Musa yayin zantawarsa da sashen hausa na Rediyo France International rfi, ya ce akwai alamar tambaya dangane da kwamitin na gwamnatin Najeriyar, yana mai cewa akwai manufar data sanya kafa kwamitin amma ba don bincike ko gano gaskiyar lamarin ba.

A lokuta da dama dai kungiyar na zargin gwamnati da kin kamanta adalci, yayinda a bangare guda suma kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke ci gaba da sukar gwamnatin kana bin da suka kira take hakki, musamman la’akari da ake ci gaba da rike jagoransu Ibrahim Zakzaky tun bayan faruwar lamarin.

Asalin Labari:

RFI Hausa

905total visits,49visits today


Karanta:  Dangote ya sayar da hannun jari mai yawa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.