Shin ko har yanzu ana amfani da biro wajen rubutu?

Tun bayan bullar sabbin hanyoyin rubutu kamar Komfuta da wayoyin salula, kasuwar alkalami ko kuma biro ta ja baya

A halin da ake ciki a yanzu, ko da sako ne mutum zai rubuta, to da sabbin hanyoyin rubutun na zamani ake amfani.

A Najeriya ma dai haka abin ya ke, domin da yawa daga cikin al’ummar kasar musamman matasa da manya ma’aikata, su kan jima ba su yi rubutu da biro ba, saboda sun fi amfani da wayoyinsu na salula ko kuma idan a wajen aiki ne da Komfuta.

Yawanci dai a yanzu dalibai ‘yan makarantun Firamare da na gaba da ita wato Sakandire ne ke amfani da biro wajen rubutu.

Masu sayar da irin abubuwan rubutu wadanda ba na zamani ba sun ce gaskia tun bayan bullar abubuwan rubutun na zamanin, kasuwarsu ta ja baya ba kamar da ba.

To amma sun ce, duk da bullar abubuwan zamanin na rubutu, dole a cigaba da amfani da biro, dan akwai abubuwa kamar zana jarrabawa.

A baya dai ba rubutu kadai ake yi da biro ba, har ma da ado, domin kuwa akan sanya shi a gaban aljihun riga musamman ga maza.

To amma yanzu al’amura sun canja, dan sau da dama zaka hadu da manyan mutane rubutu zai ta so sai kaji suna cewa ko akwai mai biro?

Asalin Labari:

BBC HAUSA

971total visits,1visits today


Karanta:  Ana daf da wancakali da Kuraye da Diloli daga Gwamnati - Aisha Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.