Shugaba Buhari na Ganawa da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar a Fadarsa

Yanzu haka shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da Manyan Hafsoshin kasar da sauran Shugabanin tsaron kasar a fadarsa gwamnati dake Aso Rock a Abuja

Ana gudanar da taron ne a ofishinsa dake cikin gidan shugaban kasa.

Wadanda suke halartar taron sun hada da Ministan tsaro, Shugaban Hukumar tsaro, Babban Hafsan Sojan Tsaron Kasar, Babban Hafsan Sojan Ruwa, Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda na Kasa, Babban Darakta Tsaro na farin kaya da Mukaddashin Shugaban Tsaro na Cikin Gida.

Wannan dai shi ne taro na farko da shugaban ke yi da manyan hafsoshin gwamnatin sa tun bayan dawowarsa daga hutun rashin lafiya a Landan

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

840total visits,2visits today


Karanta:  Daurarru 100 Sun Tsere Daga Gidan Yari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.