Shugaba Buhari ya gana da sarakunan gargajiya

Shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawa ta musamman da sarakunan gargiya na kasar nan a fadar shubagan kasa dake babban birnin Abuja.

Ganawar dai ta hada da sarakunan arewacin kasar da kuma takwararorin su na kudanci wadanda suka hada da Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Sa’ad II da Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi II.

Mataimakin shubagan kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kasance a wajen taron ganawar wanda Sarkin Zariya Alhaji Shehu Idris ya halarta.

Manyan jami’an gwamnatin tarayya sun halarci dakin ganawar, ciki har da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kari.

1252total visits,1visits today


Karanta:  Kungiyar Kananan Hukumomi A Najeriya Ta Nace Sai A Bata ‘Yancin cin Gashin Kai.

One Response to "Shugaba Buhari ya gana da sarakunan gargajiya"

  1. Bilal Sani   April 2, 2018 at 6:45 pm

    Nai Miki Murna Da Fatan Alkhairi, Kuma Kin Samu Miji Idan Zaki Iya Auren Talaka…

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.