Shugaba Buhari Ya Karbi Rahoto Kan Babachir Da Oke

Kwamitin da mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osibajo ke jagoranta ya mikawa shugaban kasa rahotan cikakken binciken da ya gudanar na zargin wata badakala da ake yiwa sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar da Ambasada Ayo Oke.

A watan Afrilu ne dai shugaban ya umarci wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakinsa ya binciki sakataren gwamnatin kasar da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA, bayan dakatar dasu bisa zarge-zarge daban-daban na almundahana.

Sai dai a bangare guda fadar shugaban ta sanar da dage zaman majalisar ministoci da ya kamata ya shugabanta a yau a karon farko cikin watanni da dama.Tun a ranar 8 ga watan Mayu ne aka shirya shugaban kasar zai karbi rahoton amma sai rashin lafiyarsa ta hana hakan, inda ya koma Landan don ganin likita ranar 7 ga watan Mayu.

A wasu rahotannin kuma:

A yau Laraba ne gwamnatin Buhari ta bayar da sanarwar dage taron da take gudanarwa na mako-mako, domin ta samu lokacin yin nazari akan wannan rahoto da aka mikawa shguaba Mohammadu Buhari, da zummar cewa cikin mako guda ‘yan Najeriya za su sami bayani kan matsayar da gwamnati za ta ‘dauka kan wannan rahoto.

Kwamitin dai ya gudanar da bincike akan zargin da ake yiwa Injiniya Lawal Babachir, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya da aka dakatarm tare da Ambasada Ayo Oke, wanda shine daraktan kula da sha’anin leken asiri na kasa da kasa wanda shima aka dakatar, bisa ga wasu makudan kudade da aka samu a wani gidansa a birnin Ikko.

Da yake magana da manema labaru Farfesa Yemi Osibanjo, ya bayar da hasken cewa lalle ya mika rahotan, amma yaki bayyana komai kan irin shawara ko abin da ke cikin rahotan, har sai an jira shugaba Buhari ya yanke hukunci akan rahotan.

A halin da ake ciki kuma shugaba Buhari na gudanar da aiki daga ofishinsa da ke cikin gidansa, a dai dai lokacin da lokacin da bayanai ke cewa ana aiki a ofishinsa da yayi sama da watanni uku ba ayi amfani da shi ba.

Karanta:  Shugaba Buhari zai koma gida daga London

 

Asalin Labari:

BBC Hausa

504total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.