Shugaba Buhari Ya Karbi Rahoto Kan Lawal Babachir da Ayo Oke

Kwamitin da mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osibajo ke jagoranta ya mikawa shugaban kasa rahotan cikakken binciken da ya gudanar na zargin wata badakala da ake yiwa sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar da Ambasada Ayo Oke.

A yau Laraba ne gwamnatin Buhari ta bayar da sanarwar dage taron da take gudanarwa na mako-mako, domin ta samu lokacin yin nazari akan wannan rahoto da aka mikawa shguaba Mohammadu Buhari, da zummar cewa cikin mako guda ‘yan Najeriya za su sami bayani kan matsalar da gwamnati za ta ‘dauka kan wannan rahoto.

Kwamitin dai ta gudanar da bincike akan zargin da ake yiwa Injiniya Lawal Babachir, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya da aka dakatarm tare da Ambasada Ayo Oke, wanda shine daraktan kula da sha’anin leken asiri na kasa da kasa wanda shima aka dakatar, bisa ga wasu makudan kudade da aka samu a wani gidansa a birnin Ikko.

Da yake magana da manema labaru Farfesa Yemi Osibanjo, ya bayar da hasken cewa lalle ya mika rahotan, amma yaki bayyana komai kan irin shawara ko abin da ke cikin rahotan, har sai an jira shugaba Buhari ya yanke hukunci akan rahotan.

A halin da ake ciki kuma shugaba Buhari na gudanar da aiki daga ofishinsa da ke cikin gidansa, a dai dai lokacin da lokacin da bayanai ke cewa ana aiki a ofishinsa da yayi sama da watanni uku ba ayi amfani da shi ba.

516total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.