Shugaba Buhari Ya Yiwa Ministoci da Na Kewaye da Shi Tankade da Rairaya-Dayabu

Kabiru Danladi na Jami'ar Ahmadu Bello yace zancen tankade da rairaya a ce ma kusan an makara. Yace tun bara ya kamata a yi kwaskwarima. Yawancin ministocin babu abun da suka yi. Idan an canzasu duk wanda ya hau ya san idan bai yi aiki ba za'a yi watsi dashi

Biyo bayan rade-radin da ake yi cewa Shugaba Buhari zai yiwa majalisar zartaswarsa garambawul, shugaban rundunar adalci ta Najeriya Abdulkarim Dayabu cewa yayi tuni ya kamata shugaban ya yiwa majalisar ministocin da na kewaye dashi tankade da rairaya.

A cewar Alhaji Abdulkarimu Dayabu shugaban rundunar adalci ta Najeriya tuni ya kamata shugaban Najeriya ya yiwa majalisar ministocinsa da ma na kewaye dashi tankade da rairaya.

Yana mai cewa tilas ne a yi wani garambawul a kowane fanni. Yace idan da Allah ya sa shugaban ya yi sa’ar mutanen da ya zaba sun zama kamar hafsan sojoji wato Janar Buratai da tafiya ta yi nisa da labari ya sha banban. Yace duk mutanen dake kewaye da shugaban wadanda suka bata kasar suka cusa masa su.

Kabiru Danladi na Jami’ar Ahmadu Bello yace zancen tankade da rairaya a ce ma kusan an makara. Yace tun bara ya kamata a yi kwaskwarima. Yawancin ministocin babu abun da suka yi. Idan an canzasu duk wanda ya hau ya san idan bai yi aiki ba za’a yi watsi dashi.

Sai dai Alhaji Bello Arabi yana mai cewa shugaban baya bukatar tankade ministocinsa sabili da irin halin da kasar da ma shugaban suka samu kansu ciki. Yana mai cewa shugaban bai samu ya zauna an yi wasu ayyuka dashi ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

393total visits,1visits today


Karanta:  Boko Haram sun dandana kudarsu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.