Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

Ana saka ran shugaba Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya a yau Asabar bayan wata jinya da ya shafe kimanin watanni uku a kasar Birtaniya ya nayi.

Shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa Birtaniyya a ranar 7 ga wayan Mayu na wannan shekarar, bayan ya mikawa mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ragamar mulki na rikon kwarya inda ya zamo mukaddashin shugaban Najeriya.

Ana saka ran Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar Litinin 21 ga watan Augusta da misalin karfe 7:00 na safe.

Buhari ya kasance mai godiya ga ‘yan Najeriya bisa karanci da suka nuna da gabatar da addo’i a yayin zaman sa a garin Landan dake kasar Birtaniyya.

A jiya ne tsohon dan takarar shugaban Kasa a Najeriya Bashir Othman ya kai masa ziyara a gidan Abuja dake Landan.

740total visits,1visits today


Karanta:  Gwamnonin Igbo Sun Haramta IPOB

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.