Shugaba Buhari zai gabatar da ayyuka daga gida sakamakon barnar beraye a ofishinsa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai shafe a kalla kusan watanni uku yana gabatar da aikinsa daga gida, bayan da beraye suka yi gagarumar barna a cikin ofishinsa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya sanar da cewar ofishin na bukatar gyara matuka bayan barnar da aka yi, musamman a banagaren kujerun zama da na’urorin sanyaya ofishin.

“Shugaban kasa na da cikakken ofis wanda aka tanadi komai a gidansa, wanda zai iya gabatar da dukkan ayyuka daga can cikin kwanciyar hankali” inji Garba Shehu.

Asalin Labari:

muryar Arewa, Daily Trust

405total visits,2visits today


Karanta:  Rikici ya barke tsakanin al'ummar Hausawa a Lagos

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.