Shugaba Muhammadu Buhari Ya Ja Kunnen Jihar Filato Kan Rikice-Rikice

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa kan kisan rashin hankalin da akayi wa mutane musamman mata da kananan yara a harin da aka kai tsakar dare a kyauyen Ancha na Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

A wata sanarwar da Babban Maitaimaka masa ta Kafofin Yada Labarai da Sadarwa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Asabar, Shugaba Buharin ya bayyana bacin ransa game da rushewar zaman lafiyar da aka fara samu a jihar.

Shugaban yayi kira ga masu ruwa da tsaki da kada su bari wannan lamarin ya lalata cigaban da jihar ta samu a baya.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin duk wani dan kasa a duk inda yake.

Ya kuma ummarci jami’an tsaro da su kamo masu hannu a wannan kisan na jihar Filato dama wadanda suka dauki nauyinsu.

Buharin yace “Ba doka bace ga duk wani mutum ko mutane su dauki doka a hannunsu da sunan daukan fansa ko ramuwar gayya, face bin hanyoyin da suka dace ta hanyar jami’an tsaro don kama duk wanda ke da hannu a kai don mika shi ya fuskanci hukunci.

“Al’umma da dama a jihar sunyi namijin kokari tare da jami’an tsaro da masu shiga tsakani don janye jihar daga rikice-rikice da kashe-kashe marasa ma’ana da suka faru a baya ta hanyar hare-hare da harin ramuwar gayya.

“Zai zama wata babbar hasara mai radadi saboda bude kofar dawowar wadannan ayyukan ta’addancin. Ina rokon daukacin al’ummar  wannan jihar  da sauran sassan kasar nan da su ringumi zaman lafiya da kuma kawo karshen irin wadannan kashe-kashe.”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

349total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.