Shugaba Muhammadu Buhari Ya Koma Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.

Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida.

Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan.

Amma a baya shugaban ya fi zuwa can don duba lafiyarsa.

Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka.

Kafin tafiyarsa, shugaban ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.

Da ma dai fadar shugaban ta ce zai je Birtaniya bayan ya kammala taron.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai a makon jiya ta ce shugaban “Zai je birnin Landan a kan hanyarsa ta komawa gida”.

Sai dai Mr Adesina bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.

A watan jiya ne dai shugaban ya koma gida Najeriya bayan ya yi doguwar jinya a Birtaniya, inda ya shafe fiye da wata uku a can.

Asalin Labari:

BBC Hausa

977total visits,2visits today


Karanta:  Sunan Muhammad Ya Samu Matsayi A Birtaniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.