Siera Leone: Zabtarewar laka ta kashe mutum 300

Akalla mutane 300 ne suka mutu a Freetown, babban birnin Saliyo, bayan da laka ta binne su a cikin gidajensu da ke wani yankin birnin.

Lamarin ya auku ne a yankin Regent da sanyin safiyar Litinin bayan ruwan sama mai kama da bakin kwarya, kuma lakar ta binne gidaje da yawa.

Wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ce da alama mutane da dama na barci a lokacin da zabtarewar lakar ya faru.

Kawo yanzu ba a san yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ba, amma mataimakin shugaban kasar Saliyo, Victor Bockarie Foh, ya ce “akwai yiwuwar daruruwan mutane sun halaka”.

Mista Foh ya fada wa Reuters cewa bala’in “ya gigita ni gaba daya”, inda ya kara da cewa an killace yankin domin gudanar da ayyukan ceto.

Kamfanin dillacin labarai na AFP na bada rahoton cewa a kalla mutum 180 suka mutu. Kawo yanzu an gano gawawwaki da dama.

Kungiyoyin masu ba da agaji na wurin domin ceto wadanda lakar ta birne a cikin gidajensu, bayan da wani bangare na dutsen ya zabtare, inji wani rahoton jaridar Sierra Leone Telegraph.

Hotunan da aka wallafa a Twitter sun nuna mutane na tafiya cikin titunan yankin cikin tabon da ya kai kugunsu bayan ruwan saman da aak yi a kusa da birnin Freetown.

A kan sami irin wannan ambaliyar ruwa a yankin birnin na Freetown, inda rashin ingantattun gine-gine kan sa ruwan ya tafi da muhallai da dama bayan ruwan sama mai yawa.

A shekarar 2015, birnin Freetown ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa bayan wata guguwar da ta hada da ruwan sama ya janyo mutuwar mutane 10 kuma dubbai suka rasa muhallansu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

550total visits,6visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.