Snapchat tayi ragista da mahukunta a Rasha ba tare da sanin ta ba

Kamfanin Snap mai mallakin manhajar Snapchat ya bayyana cewar manhajar su anyi mata ragista da mahukunta ba tare da sanin su ba kasar Rasha.

Snap ya bayyana wa BBC cewar Roskomnadzor tuni ya rattaba su a cikin tsarin na Rasha. Wannan dai zai tilastawa Snap ajiyar bayanai har na tsawon watanni shida a kasar ta Rasha inda gwamnati zata iya shiga cikin bayanan domin samun wani rahoto.

Snap ta bayyana cewar bata da wata niya ta yin hakan. Snap ta kasance kamfanin Amurka na farko da ta yi irin wannan. WhatsApp da Facebook basu yi ba har izuwa yanzu.

Sabuwar dokar ajiye bayanai ta Rasha zata fara aiki nan da kasrhen shekara inda duk wani kamfani mai launin ajiyar bayanai zaiyi ragista da mahukunta na tsahon watanni shida.

Kamfanunuwa kuma ya zama tilai su mika makullan sirri a duk sanda aka bukata, wanda yana cikin tsarin sabuwar dokar.

Yanar gizo-gizo ta VKontakte da RuTube tuni sun riga sun shiga tsarin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Gizmodo ya ruwaito.

Rashin bin dokar ka iya sa a sanyawa kamfani takunkumi. Manhajar tura sakonni ta WeChat dake kasar Sin ta samu tsaiko a farkon shekarar nan.

Snap dai bata da kididdigar masu amfani da ita a Rasha, sai dai taced akalla mutane miliyan 57 sukan yi amfani da ita daga tarayyar turai.

1137total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.