Sojin Lebanon Sun Dakatar Da Kai Wa Mayakan IS Farmaki

Rundunar Sojin Lebanon ta dakatar da kai hare-hare kan mayakan ISIS da ke kan iyakarta da kasar Syria.

Rundunar Sojin Lebanon ta dakatar da kai hare-hare kan mayakan ISIS da ke kan iyakarta da kasar Syria.

Rundunar ta ce, ta dauki matakin ne don samun wasu bayanai game da jami’anta da ISIS ta yi garkuwa da su.

Tun a ranar 19 ga watan Agusta, rundunar sojin Lebanon ta kaddamar da farmaki kan mayakan ISIS da suka yi kaka-gida a yankunan Jurud Ras Baalbek da Jurud al-Qaa da ke gabashin iyakar kasar.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin ta ce, ta dakatar da bude wuta kan mayakan don samar da hanyar cimma yarjejeniya da su, da za ta kai ga sakin sojojin Lebanon da ISIS din ta yi garkuwa da su.

Rahotanni na cewa, har yanzu akwai wasu jami’an tsaro 30 da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da ISIS ke garkuwa da su, bayan sace su da ta yi a shekarar 2014, lokacin da take kan ganiyar cin karenta babu babbaka a garin Arsal.

Rundunar Lebanon ta ce, tana matukar la’akari da jami’an nata da ke hannun ISIS, lamarin da ya tilasta mata sassauta kaddamar da farmaki kan mayakan da yawansu ya kai 600.

Kungiyar ISIS dai ta kai hare-hare da dama a ‘yan shekarun nan a Lebanon, da suka hada da tagwayen hare-heren kunar bakin wake a birnin Beirut, in da mutane 44 suka rasa rayukansu.

766total visits,58visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.