Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13

Rundunar Sojan Najeriya ta kashe fiye da ’yan kungiyar Boko Haram 13 a wani simamen da ta kai a sassan jihar Borno da Adamawa.

 

 

 

 

 

Rundunar Sojan Najeriya ta kashe fiye da ’yan kungiyar Boko Haram 13 a wani simamen da ta kai a sassan jihar Borno da Adamawa.
Mai Magana da Yawun Rundunar, Birgediya Ganar , Sani Usman shi ne ya tabbatar da lamarin a wata sanarwar da rundunar ta raba wa manema labarai a yau.
Ya bayyana cewa sojoji sun kashe ’yan ta’adda 12 yayin da rundunar ta yi musu kwantan-bauna a mahadar kauyen Miyanti-Banki a jihar Borno.
Sannan ya ce sojojin sun kashe wani dan ta’adda guda a garin Kafin Hausa da ke cikin Karamar Hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
Usman ya kara da cewa sojojin sun kashe mayakan Boko Haram da yawa a kan hanyar Dukje zuwa Mada kusa da kauyen Gulumba Gana.
“Abin bakin ciki sojojinmu biyu sun rasa rayukansu a lokacin da motarsu ta taka bam din da kungiyar Boko Haram ta binne a kan hanyar, sannan kuma sojoji hudu sun ji rauni. Tuni aka kwashe gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu tare da wadanda suka ji rauni zuwa garin Maiduguri”. Inji shi.
Ya bayyana cewa sojojin sun samu kekuna 18 da buhun fulawa 30 da buhun gyada daya da buhun siga biyu da kwandon goro biyu da fitila hudu da katan din sinadarin jusi da makamantansu.
Asalin Labari:

Aminiya

1842total visits,1visits today


Karanta:  Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.