Sultan Ya Tabbatar Cewa 1 Ga Watan Satumba Ita Ce Ranar Sallah

Mai Girma Sarkin Musulmi, Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addini Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar ya tabbatar da cewa 1 ga watan Satumba, 2017 ce ranar Babbar Sallah.

Wannan bayanin na kunshe cikin takardar da Prof. Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bada shawarwari kan harkokin Addini ta Daular Musulunci dake Sokoto ya sakawa hannu.

Sakon da kamfanin dillancin labarai na kasa ya samu ranar Laraba ya nuna cewa hakan ya biyo bayan ganin jinjirin watan Zulhijja da akayi ranar Talata.

“Kwamitin bada shawarwarin tare da kwamitin duban wata na kasa sun sami rahotanni daban-daban da suke tabbatar da ganin wata a fadin kasa bakidaya ranar Talata 22 ga watan Agusta”, kamar yadda sanarwar tace.

Sanarwar tace sakamakon hakan na nufin daukacin musulmi za su gudanar da sallar idin bana ranar Jumma’a 1 ga watan Satumba.

Sanarwar ta kara da cewa Mai Girma Sarkin Musulmi na taya daukacin musulmi murna tare da fatan yin sallah lafiya cikin walwala da kariyar Ubangiji.

Sakon ya ambato Sarkin Musulmin na karfafar guiwar yan uwa Musulmi dasu zauna lafiya da kuma yin addu’ar cigaban kasa dama duniya bakidaya. (NAN)

834total visits,1visits today


Karanta:  Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.