Super Eagles Zasu Sami N20m Daga Gurin Buhari Don Nasarar Da Sukayi; Shi Kuma Dalung Ya Yaba Musu

Ministan Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dalung ya yabawa ‘Yan Wasan Nijeriya Super Eagles don nasarar da suka samu ta 4:0 akan ‘Yan Wasan Indomitable Lions na Kasar Kamaru a wasan da suka buga a sitadiyon din Godswill Akpabio dake Uyo ranar Jumma’a don neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018.

Manyan ‘Yan Wasan Kasar zasu karbi N20m saboda kwallo 4 da suka jefa, bayan da Gwamnatin Tarayya tayi alkawarin Naira Miliyon 5 ga duk kwallo da suka jefa a wata hira jim kadan kafin karawar.

Barista Dalung ya godewa Hukumar Kwallon Kafar Kasar dama tawagar ‘yan wasan kasar saboda basu watsawa ‘yan Nijeriya kasa a ido ba duba da muhimmancin samun gurbi a wasn kwallon kafar duniya da za ayi shekara mai zuwa a kasar Rasha.

“Hukumar Kwallon Kafar Kasa na nan daram kan bakanta na ganin cewa ‘Yan Kwallon na Super Eagles sun sami gurbi shekara mai zuwa a gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya

Kunyi kokari sosai domin samun nasara haka kuma ‘yan kasa na alfahari daku saboda fitar da kasar daga kunya da kukeyi ko yaushe idan bukatar hakan ta taso.

“Mun san ciwon rashin halartar gasar cin Kofin Duniya da za ayi a Rasha shekara ta 2018. Mun baiwa Afirka muhimmanci a bagaren wasanni, kuma mun shirya don rera sauti da kuma nuna jerin abubuwan da Afirka ke yi a wasanni na duniya don haka yana da mahimmanci a garemu sosai. Bugu da kari rashin halartar Nijeriya a duk wata Gasa ta Duniya koyaushe na hanawa duniya sanin korewa da al’adar kwallon kafarmu, don haka zamu je Rasha da wani sabon salon wasan kwallon kafa,”

Karanta:  Haduran mota a bana ya halaka mutum 11,002 a Kamaru

Ministan yayi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa dama ‘yan kasa Nijeriya dasu taimakawa ‘yan wasan da addu’o’i da shawarwari masu kyau.

“Gwamnatin Tarayya zata cigaba da karfafawa ‘yan wasan guiwa saboda sadaukar da kai da sukayi ga kasarsu. Babu wani abu da zamu iya don saka musu abun da sukayi sai dai mu cigaba da nuna musu goyon baya akan wannan kokarin na zuwa kasar Rasha.

yanzu Nijeria ce ke jagorantar rukunin B da maki 9 za kuma su kara fukantar Kamarun ranar litinin a Sitadiyon din Stade Omnispirts Ahmadu Ahidjo in Yaoundé da karfe 6 na yamma.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

1035total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.