Ba ma goyon bayan raba Najeriya – Sheikh Dahiru Bauchi

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya Darikar Tijjaniyya suka yi wani babban taro a Bauchi a karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda shehunnai da halifofi da jagororin darikar daga jihohin Najeriya suka halarta da nufin bunkasa harkar ilimi da hadin kan mabiyar darikar, kuma aka yanke shawarar kafa Majalisar Koli ta Malaman Darikar Tijjaniyya a Najeriya. A karshen taron Sheikh Dahiru Bauchi ya amsa tambayoyin manema labarai kamar haka:

Ba ma goyon bayan raba Najeriya – Sheikh Dahiru Bauchi

Allah gafarta ko za ka fada mana dalilin wannan taro? Dalilin wannan taro nun kira ’yan uwanmu ’yan Tijjaniyya na Najeriya ne mu tattauna halin da muke ciki da yadda za mu shirya mafita daga matsalar da muke ciki. Babban abu dai muna kira ne don mu hada kanmu, da ma mu jama’a ce guda […]