Nijeriya Za Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya Mai Manufa Guda…. – Sultan

Nijeriya Za Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya Mai Manufa Guda…. – Sultan

Sokoto – Maigirma Sarkin Musulmi, Ahaji Sa’ad Abubakar ya roki ‘yan Nijeriya su zauna lafiya da kowa su kuma kauracewa duk wani abun da zai yi barazana ga zaman lafiyar da ke akwai tsakanin mabanbanta kabilu. Sarkin musulmin yayi wannan  kiran a wata sanarwa da Sakataren Majalisar Daular, Alhaji Umar Ladan ya fitar ranar Jumma’a […]

Shugaba Buhari ya gana da sarakunan gargajiya

Shugaba Buhari ya gana da sarakunan gargajiya

Shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawa ta musamman da sarakunan gargiya na kasar nan a fadar shubagan kasa dake babban birnin Abuja. Ganawar dai ta hada da sarakunan arewacin kasar da kuma takwararorin su na kudanci wadanda suka hada da Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Sa’ad II da Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi II. […]

Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Daga Sokoto- Maigirma Sarkin Musulmi Sultan Abubakar ya ce duk wanda yake da shirin kaiwa ‘yan kabilar Igbo mazauna arewacin kasar hari, to shi yakamata ya fara kaiwa wannan harin. Sarkin musulmin ya fadi haka ne lokacin da shugaban kabilar Igbon ta duniya, Dr Mishack Nnanta tare da rakiyar shugabannin kabilar Igbo mazuna yankin suka […]

Sarkin Musulmi Ya Jaddada Mahimancin Zaman Lafiya

A jawabinsa wa al'ummar Musulmi bayan saukowa daga babbar sallah, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya tabo batun rarrabuwan kawunan 'yan Najeriya da barazanar da hakan ke yiwa kasar kana ya jaddada mahimmancin zaman lafiya.

Sarkin Musulmi Ya Jaddada Mahimancin Zaman Lafiya

Babban abun da ya fi daukan hankalin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III a jawabinsa na babban sallah wa Musulman Najeriya shi ne irin halin da kasar Najeriya ke ciki da kalubalen rarrabuwan kawunan ‘yan kasar. Yana mai cewa kwanakin baya an samu kalamun rarrabuwa daga mutane daban daban daga sassan kasar. Ana cewa mutane […]

Sultan Ya Tabbatar Cewa 1 Ga Watan Satumba Ita Ce Ranar Sallah

Sultan Ya Tabbatar Cewa 1 Ga Watan Satumba Ita Ce Ranar Sallah

Mai Girma Sarkin Musulmi, Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addini Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar ya tabbatar da cewa 1 ga watan Satumba, 2017 ce ranar Babbar Sallah. Wannan bayanin na kunshe cikin takardar da Prof. Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bada shawarwari kan harkokin Addini ta Daular Musulunci dake Sokoto ya sakawa hannu. Sakon […]

Sarkin Musulmi Ya Kira A Mayar da Hankali Wajen Inganta Tattalin Arziki

Sarkin Muslmi Sultan Sa'ad Abubakar ya yi kira a Minna da a mayar da hankali akan habaka tattalin arziki domin inganta rayuwar al'umma da zata sa mutane ba zasu damu da wake shugabancin kasar ba.

Sarkin Musulmi Ya Kira A Mayar da Hankali Wajen Inganta Tattalin Arziki

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Sultan Sa’ad Muhammad Abubakar ya yi kira da a maida hankali wajen bunkasa tattalin arziki da zai sa ‘yan kasar su kasance cikin walwala. Yayinda yake jawabi a wani taron bunkasa kasuwanci a Minna babban birnin jihar Neja yana mai cewa kamata yayi ‘yan Najeriya su maida hankali wajen kiran […]

Facebook da Whatsapp na bata tarbiyyar ‘yan mata — Sultan

Shugaban majalisar koli ta lamurran addinin Islama a Najeriya, ya gargadi yara musamman 'yan mata da su guji daukar lokaci mai yawa kan shafukan sada zumunta na zamani domin yin hakan ka iya bata tarbiyarsu.

Facebook da Whatsapp na bata tarbiyyar ‘yan mata — Sultan

Da yake jawabi a wajen wata gasar musabakar Alkur’ani mai girma a birnin Sakkwato ranar Lahadi, Sultan Saad Abubakar, ya ce, “abin damuwa ne matuka” ganin irin yadda shafukan sada zumunta kamar su Facebook da Whatsapp da Instagram da 2go ke dauke wa yara hankali daga karatunsu. Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato shi […]

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar III da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu. Sulhun ya kai zangon karshe ne ranar Asabar da wani zaman da aka yi a birnin Sakkwato. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daya daga cikin manyan sarakuna biyu da suka jagoranci wannan sulhun […]

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

An fara sulhunta wani sabani da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad a Najeriya da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

A ranar Litinin ne dai magajin gari ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin kuma ya sanar da yin Murabus daga kan mukamin wanda ya rike tsawon shekara 20. Magajin garin dai ya yi zargin cewa sarkin ya ci masa zarafi a wajen wani sulhu da ake tsakaninsa da wani […]

Sarkin Musulmi Yayi Kira Ga ‘Yan Kasar Su Dubi Kasashen Da Ake Rikici

Sarkin Musulmi Yayi Kira Ga ‘Yan Kasar Su Dubi Kasashen Da Ake Rikici

Mai Alfarma ya bada wannan shawarar ce lokacinda yayi buda baki da shugabannin hukumomin tsaro dana kabilu. Mai-alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad na 3, yayi kira ga ‘yan Najeriya su dage wajen tabbatar da ganin kasar ta ci gaba da zama lafiya, saboda duk wani abu sabanin haka ba Alheri bane ga kasa da […]