An Bukaci Dokar Kwarmata Labarin Safarar Mutane

Hukumar yaki da fataucin mutane ta nemi mahukuntan kasar Najeriya da su samar da dokar da zata ba da daman kwarmata labarin safarar mutane tare da amincewa da bayar da tukwuici kamar yadda ake yi yanzu akan kudaden sata da makwarmata suke taimaka wa ana ganosu.

An Bukaci Dokar Kwarmata Labarin Safarar Mutane

Kakakin hukumar dake yaki da fataucin ko safarar mutane ta Najeriya Mr Josiah Emerem ya bayyana makasudin samun dokar kwarmata labarin safarar mutane. Yana mai cewa mutane da dama ba sa iya kai rahoton fataucin mutane kamar yadda a keyi da sauran laifuka. Rashin dokar na takaita ma hukumar samun rahotanni aika aikar da ake […]