Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa kimanin rayuka hudu ne aka rasa a wani sabon rikici dake neman barkewa a tsakanin Fulani Makiyaya da kabilun yankin Kwateh a yankin karamar hukumar Girei.

Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

An tabbatar da cewa rikicin na neman tashi ne biyo bayan kashe wasu Fulani makiyaya biyu, inda suma fulanin suka kashe wasu mutanen yankin biyu a wani harin daukar fansa. To sai dai tuni wannan lamarin yakai ga fara kona gidajen wasu Fulani makiyaya a yankin, kamar yadda shugaban karamar hukumar Girein Alhaji Hussaini Masta, […]

Asusun Bai Daya: NULGE Na Zargin Gwamnoni Da Babakere

Yayin da takaddamar da ake yi kan batun asusun bai daya tsakanin kanananan hukumomi da gwamnatocin jahohi da kuma batun babakere a batutuwa dabandaban da ake zargin gwamnonin jahohi da yi, a yanzu kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta shiga yin zanga-zanga.

Asusun Bai Daya: NULGE Na Zargin Gwamnoni Da Babakere

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa ta zargi gwamnonin jihohi da kin sakarwa kananan hukumomi mara wajen sarrafa kaso da suke amsa daga asusun gwamnatin tarayya, kin gudanar da sahihiyar zabe na kananan hukumomi da tauye masu hakki a matsayin masalolin da suke gurgunta harkokin gudanarwarsu. Wannan bayanin na kunshe cikin takardar da shugaban kungiyar […]

An dauki tsauraran matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba domin babar Sallah

Rarraba Dubi ra’ayoyi An dauki tsauraran matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba domin bukukuwan babar sallah.

An dauki tsauraran matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba domin babar Sallah

 An dauki tsauraran matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba domin bukukuwan babar sallah. Yayin da al’ummar Musulmi ke shirye shiryen babbar Sallah,rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba na nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro domin ganin an gudanar da bukukuwan sallar cikin tsanaki.inda aka kara baza jami’an tsaro a cikin shirin ko ta […]

’Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu a Adamawa

’Yan Kungiyar Boko Haram sun sake kai hari tare da kone kauyukan Muduvu da Nyibango da ke cikin Karamar Hukumar Madagali a jihar Adamawa.

’Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu a Adamawa

’Yan Kungiyar Boko Haram sun sake kai hari tare da kone kauyukan Muduvu da Nyibango da ke cikin Karamar Hukumar Madagali a jihar Adamawa. Harin ya auku ne bayan ’yan kwanaki da kai irinsa a kauyukan Ghumbili da Mildu inda mutane da dama suka bata. Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Malam Yusuf Muhammed ya fada wa […]

‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a jihar Adamawa

‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a jihar Adamawa

‘Yan Boko Haram sun tura hari  a uguyoyi uku a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa. Yan ta’addar suna nema su maida Adamawa kamar yadda sukayi wa Jahar Maiduguri. Sun kai harin ne a  karamar hukumar Mildu wanda har mutane bakwai suka rasa rayukansu. Sun sake kai hari a jahohin Muduvu da Nyibango. Daga bakin  […]

Adamawa: Boko Haram Ta Kone Garin Yumbuli Kurmus

A wani mummunan hari da Boko Haram ta kai yankin Madagali ta kwashi awa uku tana kone garin Yumbuli inda babu abun da ta bari kuma duk mutanen garin da suka tsere kayan jikinsu ne kawai dasu, garin kuma ya zama toka gaba daya saboda hatta dabbobi basu tsira ba.

Adamawa: Boko Haram Ta Kone Garin Yumbuli Kurmus

Rahotanni da muka samu da dumi duminsu na cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun kone garin Yumbuli kurmus. Garin Yumbuli yana cikin karamar hukumar Madagali ne kuma yana kan iyaka da dajin Sambisa inda ‘yan Boko Haram suka yi kakagida. Harin na yau shi ne na hudu cikin mako guda da ‘yan Boko Haram zasu […]

Ana Zargin Sojoji da Cin Zarafin Jama’a a Naurar Banki ta ATM a Yola

Farar hula dake mu’amala da bankunan kasuwanci a Yola fadar jihar Adamawa suna kokawa da abinda suka kira cin fuska da cin mutunci da kananan jami’an soja ke yi masu a injunan bankuna na cire kudi ko ATM dake harabobin bankuna.

Ana Zargin Sojoji da Cin Zarafin Jama’a a Naurar Banki ta ATM a Yola

Wakilin Sashen Hausa ya ci karo da irin wannan lamarin a daya daga cikin bankunan kasuwanci inda hatsaniya ta kaure tsakanin wata matar aure goye da jariri da kuma yaro dan kasa da shekara shida da wani karamin jami’in soja da ya ki bin layi duk da cewa ya tarar da wasu mutane a layi […]

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13

Rundunar Sojan Najeriya ta kashe fiye da ’yan kungiyar Boko Haram 13 a wani simamen da ta kai a sassan jihar Borno da Adamawa.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13

          Rundunar Sojan Najeriya ta kashe fiye da ’yan kungiyar Boko Haram 13 a wani simamen da ta kai a sassan jihar Borno da Adamawa. Mai Magana da Yawun Rundunar, Birgediya Ganar , Sani Usman shi ne ya tabbatar da lamarin a wata sanarwar da rundunar ta raba wa manema labarai […]

Wasu ‘Yanbindiga Sun Yiwa Mutane Yankan Rago a Midul, Adamawa

Yayinda ake zaton hare-haren ta'addanci ya ragu sai gashi a daren jiya wasu 'yanbinda da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yiwa mutane yankan rago a Midul cikin karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa

Wasu ‘Yanbindiga Sun Yiwa Mutane Yankan Rago a Midul, Adamawa

Wasu ‘yanbindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun yiwa wasu yankan rago a garin Midul dake cikin karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa Arewa maso gabashin Najeriya. Rahotanni na cewa ‘yan bindiga sun yi shigan burtu ne cikin dare inda suka farma kauyen mai tazaran kilomita ko zuwa bakwai zuwa garin […]

Jam’iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Jam’iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP reshen jihar Adamawa ta bayyana cewar zata tuntubi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar domin dawo dashi cikin jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar reshen na Adamawa Alhaji Abdulrahman Bobboi ya bayyana hakan a yayin da yake amsa tambayoyi ga ‘yan jarida a wajen wani taro a garin Yola dake jihar Adamawa. […]