Kotun ICC Ta Yanke Hukuncin Diyyar Tumbuktu

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta zartas da hukuncin biyan diyyar Yuro milyan 2 da digo 7 na barnar da Mayakan Mali suka tafka a birnin Tumbuktu mai dogon tarihi sakamakon rushe kaburburan manyan Shehunnai a shekarar 2012.

Kotun ICC Ta Yanke Hukuncin Diyyar Tumbuktu

Tun a watan Satumbar bara ne dai kotun ta yankewa mutumin daya jagoranci lalata Kaburburan Shehunnan Ahmad al-Faqi al-Mahdi hukuncin daurin shekaru 9 a gidan yari, sai dai a hukuncin da alkalin ya yanke yau, ya ce ya ragewa asusun amintattu na masu laifi su yanke nawa ya kamata ya biya. Tun a shekarar 2004 […]