ADAMAWA: Maharban Dake Taimakawa a Yaki da Boko Haram Sun Yi Barazanar Janyewa

Hadakar kungiyar yan sakai na maharba a Najeriya sun gudanar da wani taron gaggawa a jihar Adamawa don gano hanyoyin magance matsalolin da suka yi mata tarnakaki a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.

ADAMAWA: Maharban Dake Taimakawa a Yaki da Boko Haram Sun Yi Barazanar Janyewa

A taron wasu ‘ya’an kungiyar da dama sun nemi da ta janye daga bakin daga a taimakawa dakarun sojin Najeriya da ‘yan sakan ke yi a yanzu a yaki da ‘yan Boko Haram sakamakon abun da suka kira ko in kulan da suke zargin gwamnatocin jihohi ke nuna musu Yayin dai wannan taron gaggawa da […]