Al-Shabaab ta kama wani yanki mai arzikin uranium a Somalia

Gwamnatin Somalia ta bukaci taimakon gaggawa daga Amurka na ta hana mayakan kungiyar al-Shabaab samar da makamashin Uranium da ake hada makamin kare dangi da shi, ga kasar Iran.

Al-Shabaab ta kama wani yanki mai arzikin uranium a Somalia

A wata wasika da ministan harkokin kasashen waje na Somalia, Yusuf Garaad ya aika wa Washington, ya ce al-Shabaab ta kama wani yanki da ke da tarin sinadarin na Uranium kuma tuni ta fara aikin hako shi. A wani bincike da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta taba yi, ta ce Somalia na […]