Alhazai Na Fuskantar matsaloli iri daban-daban A Mina

Ana daf da fara dawo da Alhazan Najeriya, Alhazan ke fuskantar matsalolin iri daban-daban da suka hada da wurin kwana da kuma wurin kewaya wa.

Alhazai Na Fuskantar matsaloli iri daban-daban A Mina

Yayin da ake haramar dawowa daga aikin Hajjin bana, Alhazan Najeriya dake Mina suna fuskantar matsalolin wurin kwana da kuma wurin kewayawa. Wannan yasa wasu da yawa suke kwana waje, yayinda wasu da yawa kuma sai sun shiga dogon layi kafin su samu damar kewaya wa. Wannan lamarin ya fito fili ne lokacin da shugaban hukumar Alhazan Najeriya Barister Abdullahi Mukthar […]

Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya

Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya

Wasu alhazan Najeriya bakwai sun mutu a Saudiyya gabanin a fara aikin Hajji.Alhazan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna. Sannan wata Hajiya daga Jihar Kogi ta Haihu a Madina. Shugaban NAHCON Abdullahi Mukhtar, ya ce za a hukunta jihar da matar ta fito ta hanyar rage mata kujeru […]

An fara jigilar Alhazai a Nigeria

An fara jigilar Alhazai a Nigeria

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta ce ta fara jigilar maniyya aikin hajjin bana a Najeriya inda alhazai suka fara tashi daga shiyyar Abuja ranar Lahadi. Shugaban hukumar Abdullahi Muktar ya shaida wa BBC cewa “an yi sahun farko daga Abuja inda aka kwashe alhazai 480 da misalin karfe 3:16 na ranar Lahadi.” Ya ce ana […]