Sanata Wamakko ya tsallake rijiya da baya bayan ruftawar gidansa

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato a Najeriya Aliyu Magatakarda Wamakko, ya tsallake rijiya da baya ranar Lahadi da daddare, bayan wani sashe na gidansa ya rufta.

Sanata Wamakko ya tsallake rijiya da baya bayan ruftawar gidansa

Mai magana da yawun Sanata Wamakko, wanda a yanzu dan majalisar dattawan kasar ne, ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni. Alhaji Bashir Mani ya ce lamarin ya faru ne jim kadan da ficewar Sanata Wamakko daga gidan wanda ke a unguwar masu-hannu-da-shuni ta […]