Burkina Faso: An kashe mutum 17 a Ouagadougou

Rahotanni sun ce da misalin karfe 12:00 daren Lahadi aka fara ji tashin harbin bindiga a wani gidan cin abincin Turkawa da ake kira da Aziz Istanbul Restaurant, a birnin na Oaugadougou.

Burkina Faso: An kashe mutum 17 a Ouagadougou

Gwamnatin kasar ta ce kawo yanzu mutum 17 ne suka mutu a harin sannan 8 sun samu raunuka. Tuni kuma jami’an tsaro suka killace yankin da al’amarin ya auku. Wurin dai bai shi da tazara sosai da wani otal da kuma wani wurin shan shayi da aka taba kai irin wannan hari a watan Janairun […]