‘Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Mayakan Boko Haram fiye da 240 ne suka mika wuya, bayan farmaki ta sama da kasa da dakarun hadin guiwa na kasa da kasa (MNJTF) suka kai a maboyarsu.

‘Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Wata sanarwa da rundunar ta MNJTF ta fitar, ta bayyana cewa yawancin mayakan sun fito ne daga yankin na tafkin Chadi. Ta kara da cewa mayakan sun mika wuyan ne a sashe na biyu na sansanin soja a yankin Bagasola da ke kasar Chadi. Dakarun na MNJTF da suka fito daga Najeriya, Chadi, Nijar da […]