Yadda fasto ya kare Musulmi 2000 a cocinsa

Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar hari daga kungiyar gwagwarmayar Kristoci ta anti-Balaka.

Fasto Juan José Aguirre Munoz ya ce Musulmin ‘yan gudun hijiran ba za su bar harabar cocinsa ba a birnin Bangassou da ke kudu-maso-gabashin kasar, sai bayan ya samu tabbaci kan tsaron rayukansu. Ya ce Musulmin da ya ba mafaka suna “fuskantar barazanar kisa” ne daga wurin mambobin kungiyar anti-Balaka. Wani babban jami’in Majalisar Dinkin […]