An Zargi ‘Yan Rohingya Da Kashe ‘Yan Hindu

Rundunar sojan Bama ta zargi Musulmi 'yan ta-da-kayar-baya na Rohingya da kashe mace 20 da namiji takwas har ma da yara, wadanda ta ce ta gano gawawwakinsu a wani makeken kabari.

An Zargi ‘Yan Rohingya Da Kashe ‘Yan Hindu

Sojojin sun ce gawawwakin da suka gano na ‘yan Hindu ne, wadanda dubbansu ke cewa ‘yan ta-da-kayar-bayan sun tilasta musu tserewa daga kauyukansu. Ba a dai iya tantance sahihancin wannan bayani na rundunar sojan Myanmar ba. Musulmai ‘yan Rohingya dubu 430 ne suka gudu daga Myanmar zuwa Bangladesh, sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa […]

Buhari Ya Bukaci Kawo Karshen Kisan Kare Dangi a Myanmar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi Allah-wadai da kisan kare dangin da sojojin Myanmar ke yi wa ‘yan kabilar Rohingya, akasarinsu Musulmi.

Buhari Ya Bukaci Kawo Karshen Kisan Kare Dangi a Myanmar

Buhari ya bukaci haka ne a yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72 da aka fara gudanarwa a birnin New York na Amurka. Buhari ya alakanta rikicin jihar Rakhine ta Myanmar da kisan kare dangin da aka gani a Bosnia a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994. Shugaba […]

Mutanen Rohingya Ba ‘Yan Kasa Bane – Sojin Myanmar

Rundunar sojin Myanmar ta bukaci hadin-kan al’ummar kasar wajen bayyana wa duniya ainihin tushen ‘yan kabilar Rohingya.

Mutanen Rohingya Ba ‘Yan Kasa Bane – Sojin Myanmar

Rundunar ta ce, mutanen Rohingya ba su da asali a kasar, kuma tana kai mu su hari ne don kakkabe masu dauke makamai da ke cikinsu wadanda ta kira da ‘yan tawaye. Rundunar Sojin Myanmar ta bayyana cewa, tana kaddamar da hare-haren ne a yankin arewacin jihar Rakhine da zimmar kakkabe ‘yan tawayen na Rohingya […]

Gwamnatin Bangladesh zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijirar Rohingya

Gwamnatin Bangladesh zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijirar Rohingya

Bangladesh ta ce, zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijira na kabilar Rohingya da suke shigo mata, bayan tserewa daga Myanmar. ‘Yan sandan kasar sun ce tilas ne ‘yan gudun hijirar na Kabilar Rohingya, su zauna a sansanonin wucin gadin da gwamnati ta basu a maimakon fantsama cikin kasar. Gwamnatin Bangladesh ta kuma sanar da shirinta […]

Musulman Rohingya Dubu 60 Sun Nemi Mafaka a Bangladesh

Tuni dai Hukumar bada tallafin abinci ta duniya ta dakatar da bada tallafin abincin ga jihar ta Rakhine mai fama da rikicin.

Musulman Rohingya Dubu 60 Sun Nemi Mafaka a Bangladesh

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akalla Musulman Rohingya dubu 60 ne suka tsere zuwa Bangladesh a cikin kwanaki takwas sakamakon rikicin da ake fama da shi a jihar Rakhine da ke Myanmar. Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Vivian Tan ta shaida wa kamfanin Dillancin labaran Faransa na […]