Dalilin da ya sa na fito a Barauniya – Hafsa Idris

Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin "Barauniya" shi ya sa ta taka rawa sosai a fim din kamar yadda gogaggun barayi ke yi.

Dalilin da ya sa na fito a Barauniya – Hafsa Idris

Hafsa, wacce ake kira ‘Barauniya’ ko ‘Yar Fim a Kannywood, ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza. Ta kara da cewa, “Yin fim ya fi aikin gwamnati domin kuwa abin da nake samu ma’aikacin gwamnati ba zai samu ba.” Da fim nake yin hidimomina da na iyayena […]