‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Wata 'yar jarida daga arewa maso gabashin Najeriya ce ta lashe lambar yabo ta BBC ta Komla Dumor ta bana.

‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Amina Yuguda mai gabatar da labarai ce a gidan talbijin na Gotel da ke Yola, inda ta gabatar da labarai da dama har da wadanda suka shafi rikicin Boko Haram. Za ta fara aikin koyon sanin makamar aiki na tsawon wata uku a London cikin watan Satumba. An kirkiro lambar yabon ne don girmama Komla […]